Fit 33:21-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen.

22. A sa'ad da zatina yake wucewa, zan sa ka a tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har in wuce,

23. sa'an nan in ɗauke hannuna, za ka kuwa ga bayana, amma ba za ka ga fuskata ba.”

Fit 33