Fit 30:1-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Za ku yi bagaden ƙona turare. Za ku yi shi da itacen ƙirya.

2. Tsawonsa da fāɗinsa kamu guda guda ne, zai zama murabba'i, amma tsayinsa ya zama kamu biyu. Za a haɗa zankayensa su zama ɗaya da shi.

3. Za ku dalaye shi, da bisansa, da gyaffansa, da zankayensa da zinariya tsantsa. Ku kuma yi masa dajiyar zinariya.

4. Za ku yi masa ƙawanya biyu na zinariya a ƙarƙashin dajiyar gefe da gefe, daura da juna. Ƙawanen za su zama inda za a zura sandunan ɗaukarsa.

5. Za ku yi sandunan da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya.

6. Sai ku ajiye bagaden a gaban labulen akwatin alkawari da murfin akwati inda zan sadu da kai.

7. Haruna kuwa zai ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kowace safiya lokacin da yake gyarta fitilun.

8. Zai kuma ƙona turaren sa'ad da ya kunna fitilun da almuru. Za a riƙa ƙona turare kullum a gaban Ubangiji dukan zamananku.

9. Ba za a ƙona wani irin turare dabam ba a bisansa, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta gari, ko ta sha, a bisansa ba.

10. Sau ɗaya a shekara Haruna zai yi kafara a bisa zankayensa. Zai yi kafara a bisansa da jinin hadaya don zunubi ta yin kafara. Za a riƙa yin wannan dukan zamananku, gama bagaden mai tsarki ne ga Ubangiji.”

11. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa,

12. “A sa'ad da za ku ƙidaya Isra'ilawa, sai ko wannensu ya biya fansar kansa ga Ubangiji domin kada annoba ta buge su lokacin da za ku ƙidaya su.

13. Dukan wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar kuwa zai biya kuɗi bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Tilas kowanne ya biya wannan, gama sadaka ce ga Ubangiji.

14. Duk wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar tun daga mai shekara ashirin ko fi, zai ba da wannan sadaka ga Ubangiji.

15. Lokacin da kuke ba da wannan sadaka ga Ubangiji saboda kafarar rayukanku, mai samu ba zai zarce ba, matalauci kuma ba zai ba da abin da ya gaza abin da aka ƙayyade ba.

16. Za ku karɓi kuɗin nan na kafara daga wurin Isra'ilawa, ku ajiye shi domin aiki a alfarwa ta sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar kansu.”

17. Ubangiji ya kuma ce wa Musa,

Fit 30