Fit 3:21-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. “Zan sa wannan jama'a su yi farin jini a idanun Masarawa, sa'ad da kuka fita kuma, ba za ku fita hannu wofi ba.

22. Amma kowace mace za ta roƙi maƙwabciyarta da wadda take cikin gidanta kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, za ku sa wa 'ya'yanku mata da maza. Da haka za ku washe Masarawa.”

Fit 3