Fit 24:8-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Musa kuwa ya ɗauki jinin ya watsa wa jama'ar. Sa'an nan ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, wanda yake cikin dokokin nan duka.”

9. Musa ya haura tare da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawan nan saba'in na Isra'ila.

10. Suka ga Allah na Isra'ila. Wurin da yake ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama.

11. Amma Ubangiji bai yi wa dattawan Isra'ila wani abu ba, ko da yake suka ga zatin Allah. Su kuma suka ci suka sha a gaban Allah.

12. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka hawo zuwa wurina a bisa dutsen, ka zauna har in ba ka allunan dutse da yake da dokoki da farillan da na rubuta don a koya musu.”

13. Sai Musa ya tashi, shi da baransa Joshuwa, suka tafi, suka hau dutsen Allah.

Fit 24