Fit 24:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ku zo wurina, kai, da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawa saba'in na Isra'ila. Ku yi sujada daga nesa kaɗan.

2. Musa ne kaɗai zai kusaci Ubangiji. Amma sauran kada su zo kusa, kada kuma jama'a su hau tare da shi.”

3. Musa ya tafi, ya faɗa wa jama'a dukan dokokin Ubangiji da ka'idodinsa, sai dukan jama'a suka amsa gaba ɗaya, suka ce, “Za mu kiyaye dukan dokokin da Ubangiji ya ba mu.”

4. Musa kuwa ya rubuta dukan dokokin Ubangiji. Kashegari da sassafe ya gina bagade a gindin dutsen, da kuma ginshiƙai goma sha biyu bisa ga yawan kabilai goma sha biyu na Isra'ila.

Fit 24