5. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ɗauki waɗansu dattawa daga cikin jama'ar Isra'ila, ka wuce a gaban jama'ar. Ka kuma ɗauki sandanka wanda ka bugi Nilu da shi, ka tafi.
6. Zan tsaya a dutsen Horeb can a gabanka. Za ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito domin jama'a su sha.” Musa kuma ya yi haka nan a gaban dattawan Isra'ila.
7. Sai aka sa wa wurin suna, “Masaha” da “Meriba”, saboda Isra'ilawa suka yi husuma, suka kuma jarraba Ubangiji suna cewa, “Ubangiji yana tare da mu, ko babu?”
8. Amalekawa suka zo su yi yaƙi da Isra'ilawa a Refidim.