Fit 17:13-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Joshuwa kuwa ya ragargaza rundunar Amalekawa da takobi.

14. Ubangiji ya ce wa Musa, “Rubuta wannan a littafi domin a tuna da shi, ka kuma faɗa wa Joshuwa zan shafe Amalekawa ɗungum.”

15. Sai Musa ya gina bagade ya sa masa suna, Yahweh Nissi, wato Ubangiji ne tutarmu.

Fit 17