Fit 17:12-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sa'ad da hannuwan Musa suka gaji, Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka ajiye wa Musa, ya zauna a kai, su kuwa suka tsaya a gefen damansa da hagunsa suna tallabe da hannunsa sama, suka tallabe su har faɗuwar rana.

13. Joshuwa kuwa ya ragargaza rundunar Amalekawa da takobi.

14. Ubangiji ya ce wa Musa, “Rubuta wannan a littafi domin a tuna da shi, ka kuma faɗa wa Joshuwa zan shafe Amalekawa ɗungum.”

15. Sai Musa ya gina bagade ya sa masa suna, Yahweh Nissi, wato Ubangiji ne tutarmu.

16. Ya ce, “Ubangiji ya tabbata zai yaƙi Amalekawa har abada.”

Fit 17