8. Sa'an nan dukan fādawanka za su zo wurina su fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama'arka!’ Sa'an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna a husace.
9. Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir'auna ba zai kasa kunne gare ka ba, sai na ƙara aikata waɗansu mu'ujizai cikin ƙasar Masar.”
10. Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu'ujizai a gaban Fir'auna. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, bai kuwa saki Isra'ilawa daga ƙasarsa ba.