4. Musa ya ce wa Fir'auna, “Ga abin da Ubangiji ya faɗa, ‘A wajen tsakar dare zan ratsa cikin Masar.
5. Kowane ɗan farin da yake ƙasar Masar zai rasu, daga ɗan farin Fir'auna wanda zai hau gadon sarautarsa, har zuwa ɗan farin kuyanga wadda take niƙa, da dukan ɗan farin shanu.
6. Za a kuwa yi kuka mai zafi ko'ina a ƙasar Masar irin wanda ba a taɓa yi ba, ba kuma za a ƙara yi ba.
7. Amma ko kare ba zai yi wa wani mutum ko dabba na Isra'ila haushi ba, domin ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masarawa da Isra'ilawa.’
8. Sa'an nan dukan fādawanka za su zo wurina su fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama'arka!’ Sa'an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna a husace.