1. Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yanzu dai zan ƙara bugun Fir'auna da Masarawa sau ɗayan nan kawai da annoba. Bayan wannan zai sake ku. Sa'ad da ya bar ku ku tafi, zai iza ƙyeyarku.
2. Sai ka faɗa wa jama'a, kowane mutum da kowace mace su roƙi kayan ado na azurfa da na zinariya daga wurin maƙwabtansu.”
3. Ubangiji kuwa ya sa jama'a su yi farin jini a idanun Masarawa. Musa kuwa ya zama babban mutum a ƙasar Masar a gaban fādawan Fir'auna da kuma gaban jama'ar.
4. Musa ya ce wa Fir'auna, “Ga abin da Ubangiji ya faɗa, ‘A wajen tsakar dare zan ratsa cikin Masar.
5. Kowane ɗan farin da yake ƙasar Masar zai rasu, daga ɗan farin Fir'auna wanda zai hau gadon sarautarsa, har zuwa ɗan farin kuyanga wadda take niƙa, da dukan ɗan farin shanu.
6. Za a kuwa yi kuka mai zafi ko'ina a ƙasar Masar irin wanda ba a taɓa yi ba, ba kuma za a ƙara yi ba.