Fit 11:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yanzu dai zan ƙara bugun Fir'auna da Masarawa sau ɗayan nan kawai da annoba. Bayan wannan zai sake ku. Sa'ad da ya bar ku ku tafi, zai iza ƙyeyarku.

2. Sai ka faɗa wa jama'a, kowane mutum da kowace mace su roƙi kayan ado na azurfa da na zinariya daga wurin maƙwabtansu.”

Fit 11