Fit 1:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗannan su ne sunayen 'ya'ya maza na Isra'ila, waɗanda suka tafi Masar tare da Yakubu, kowanne da iyalinsa.

2. Su ne Ra'ubainu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza,

3. da Issaka, da Zabaluna, da Biliyaminu,

4. da Dan, da Naftali, da Gad, da Ashiru.

5. Zuriyar Yakubu duka mutum saba'in ne, Yusufu kuwa, an riga an kai shi Masar.

6. Ana nan sai Yusufu ya rasu, shi da dukan 'yan'uwansa na wannan tsara.

7. Amma 'ya'yan Isra'ila suka hayayyafa, suka ƙaru ƙwarai, suka riɓaɓɓanya, suka ƙasaita ƙwarai da gaske, har suka cika ƙasar.

8. A wannan lokaci kuwa aka yi wani sabon sarki a Masar wanda bai san Yusufu ba.

Fit 1