Filib 1:22-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. In ya zamanto rayuwa zan yi a cikin jiki, to, zan yi aiki mai amfani ke nan. Amma na rasa abin da zan zaɓa.

23. Duka biyu suna jan hankalina ƙwarai. Burina in ƙaura in zauna tare da Almasihu, domin wannan shi ne ya fi kyau nesa.

24. Amma in wanzu a cikin jiki, shi ya fi wajabta saboda ku.

Filib 1