Filib 1:15-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Lalle waɗansu suna wa'azin Almasihu saboda hassada da husuma, amma waɗansu kam, saboda kyakkyawar niyya ne.

16. Waɗannan suna yi ne a kan ƙauna, sun sani, an sa ni nan ne domin kāriyar bishara.

17. Waɗancan kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin ɗaurina.

18. Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Almasihu, na kuma yi farin ciki da haka. I, zan yi farin ciki kuwa.

19. Domin na san duk wannan zai zama sanadin lafiyata, ta wurin addu'arku da taimakon Ruhun Yesu Almasihu.

20. Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin hali matuƙa a yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko ta wurin rayuwata, ko ta wurin mutuwata.

21. Domin ni, a gare ni, rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce.

22. In ya zamanto rayuwa zan yi a cikin jiki, to, zan yi aiki mai amfani ke nan. Amma na rasa abin da zan zaɓa.

Filib 1