8. Haka nan kuwa dukan kwanakin Shitu shekara ce ɗari tara da goma sha biyu, ya rasu.
9. Da Enosh ya yi shekara tasa'in, ya haifi Kenan.
10. Bayan Enosh ya haifi Kenan ya rayu shekara ɗari takwas da goma sha biyar, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
11. Haka nan kuwa dukan kwanakin Enosh shekara ce ɗari tara da biyar, ya rasu.
12. Sa'ad da Kenan ya yi shekara saba'in, ya haifi Mahalalel.
13. Bayan da Kenan ya haifi Mahalalel ya yi shekara ɗari takwas da arba'in, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
14. Haka nan kuwa dukan kwanakin Kenan shekara ce ɗari tara da goma, ya rasu.
15. Sa'ad da Mahalalel ya yi shekara sittin da biyar ya haifi Yared.
16. Bayan da Mahalalel ya haifi Yared, ya yi shekara ɗari takwas da talatin, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
17. Haka nan kuwa dukan kwanakin Mahalalel shekara ce ɗari takwas da tasa'in da biyar, ya rasu.
18. Sa'ad da Yared ya yi shekara ɗari da sittin da biyu, ya haifi Anuhu.