Far 41:20-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sai ramammun, munanan shanun suka cinye shanun nan bakwai masu ƙiba na farko,

21. amma da suka haɗiye su, ba wanda zai iya sani sun haɗiye su, gama suna nan a ramammunsu kamar yadda suke a dā. Sai na farka.

22. Har yanzu kuma, a cikin mafarkina ga zangarku masu kauri kyawawa guda bakwai, suna girma a kara guda,

Far 41