1. Aka kuwa gangara da Yusufu zuwa Masar. Sai Fotifar Bamasare sarkin yaƙin Fir'auna, shugaban masu tsaron fāda ya saye shi daga hannun Isma'ilawa, waɗanda suka gangaro da shi zuwa can.
2. Ubangiji yana tare da Yusufu, har ya zama mutum ne mai galaba a gidan maigidansa Fotifar, Bamasaren.
3. Maigidansa kuwa ya ga Ubangiji yana tare da shi, Ubangiji kuma yakan sa albarka ga aikin hannuwansa duka.
4. Don haka Yusufu ya sami tagomashi a wurinsa, ya zama mai yi masa hidima. Fotifar kuma ya shugabantar da shi a bisa gidansa, da bisa dukan abin da yake da shi.