3. Isra'ila kuwa ya fi ƙaunar Yusufu da kowannensu, domin shi ɗan tsufansa ne. Sai ya yi masa riga mai ado.
4. Amma sa'ad da 'yan'uwansa suka gane mahaifinsu yana ƙaunarsa fiye da dukansu, suka ƙi jininsa, ba su iya maganar alheri da shi.
5. Yusufu ya yi mafarki. Sa'ad da ya faɗa wa 'yan'uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.
6. Ya ce musu, “Ku ji irin mafarkin da na yi.
7. Ga shi, muna ɗaurin dammuna cikin gona, ga kuwa damina ya tashi tsaye kyam, ga kuma dammunanku suka taru kewaye da shi, suka sunkuya wa damina.”