24. 'Ya'yan Rahila, su ne Yusufu da Biliyaminu.
25. 'Ya'yan Bilha, kuyangar Rahila, su ne Dan da Naftali.
26. 'Ya'yan Zilfa, kuyangar Lai'atu, su ne Gad da Ashiru. Waɗannan su ne 'ya'yan Yakubu da aka haifa masa a Fadan-aram.
27. Yakubu kuma ya zo wurin mahaifinsa a Mamre, a Kiriyat-arba, wato Hebron ke nan, inda Ibrahim da Ishaku suka yi baƙunci.
28. Yanzu kuwa kwanakin Ishaku shekara ce ɗari da tamanin.