Far 30:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Rahila ta ga ba ta haihuwa, sai ta ji kishin 'yar'uwarta, ta kuma ce wa Yakubu, “Ka ba ni 'ya'ya, in kuwa ba haka ba, zan mutu!”

2. Fushin Yakubu ya yi ƙuna a kan Rahila, ya ce, “Ina daidai da Allah ne, wanda ya hana ki haihuwa?.”

Far 30