Lai'atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra'ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.”