Far 27:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Lokacin da Ishaku ya tsufa, idanunsa kuma suka yi duhu har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa, ya ce masa, “Ɗana!”Sai ya amsa, “Ga ni nan.”

2. Ishaku ya ce, “Ga shi, na tsufa, ban san ranar rasuwata ba.

3. Yanzu fa, ka ɗauki makamanka, da kwarinka da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama,

4. ka shirya mini abinci mai daɗi irin wanda nake so, ka kawo mini in ci, don in sa maka albarka kafin in rasu.”

5. Rifkatu kuwa tana ji lokacin da Ishaku yake magana da ɗansa Isuwa. Don haka, sa'ad da Isuwa ya tafi jeji garin ya farauto nama ya kawo,

6. sai Rifkatu ta ce wa ɗanta Yakubu, “Na ji mahaifinka ya yi magana da ɗan'uwanka Isuwa, ya ce,

7. ‘Kawo mini nama, ka shirya mini abinci mai daɗi in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in rasu.’

8. Yanzu fa, ɗana, ka biye wa maganata yadda zan umarce ka.

9. Je ka garke, ka kamo 'yan awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi da su domin mahaifinka, irin wanda yake so.

Far 27