8. Amma idan matar ba ta yarda ta biyo ka ba, ka kuɓuta daga rantsuwan nan tawa. Kai dai kada ka koma da ɗana can.”
9. Sai baran ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar Ibrahim maigidansa, ya kuwa rantse masa zai yi.
10. Baran ya ɗibi raƙuma goma daga cikin raƙuman maigidansa. Ya tashi, yana ɗauke da tsaraba ta kowane irin abu mai kyau na maigidansa a hannunsa. Ya kama hanyar Mesofotamiya zuwa birnin Nahor.
11. Ya durƙusar da raƙumansa a bayan birnin, kusa da bakin rijiyar ruwa da maraice, wato lokacin da mata sukan tafi ɗebo ruwa.
12. Sai ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim.
13. Ga shi kuwa, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ga kuma 'yan matan mutanen birnin suna fitowa garin ɗibar ruwa.
14. Bari budurwar da zan ce wa, ‘Ina roƙo, ki sauke tulunki domin in sha,’ wadda za ta ce, ‘Sha, zan kuma shayar da raƙumanka,’ bari ta zama ita ce wadda ka zaɓa wa baranka Ishaku. Ta haka zan sani ka nuna madawwamiyar ƙaunarka ga maigidana.”
15. Kafin ya rufe baki, sai ga Rifkatu wadda aka haifa wa Betuwel ɗan Milka, matar Nahor ɗan'uwan Ibrahim, ta fito da tulun ruwanta a bisa kafaɗarta.
16. Budurwa mai kyan tsari ce. Tana da kyan gani ƙwarai, budurwa ce, ba wanda ya taɓa saninta. Ta gangara zuwa rijiyar ta cika tulunta, ta hauro.
17. Sai baran ya tarye ta a guje, ya ce, “Roƙo nake, ki ba ni ruwa kaɗan daga cikin tulunki in sha.”
18. Ta ce, “Sha, ya shugabana.” Nan da nan ta sauke tulunta ta riƙe a hannunta, ta ba shi ya sha.
19. Sa'ad da ta gama shayar da shi, ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka kuma, har su gama sha.”
20. Sai nan da nan ta bulbule tulunta a cikin kwami, ta sāke sheƙawa a guje zuwa rijiyar, ta kuwa ɗebo wa raƙumansa duka.
21. Mutumin kuwa ya zura mata ido, shiru, yana so ya sani ko Allah ya arzuta tafiyarsa, ko kuwa babu?
22. Sa'ad da raƙuman suka gama sha, mutumin ya ɗauki zoben zinariya mai nauyin rabin shekel, ya sa mata a hanci. Ya kuma ɗauki mundaye biyu na shekel goma na zinariya ya sa a hannuwanta,
23. ya ce, “Ki faɗa mini ke 'yar gidan wace ce? Akwai masauki a gidan mahaifinki inda za mu sauka?”
24. Sai ta ce masa, “Ni 'yar Betuwel ce ɗan Milka wanda ta haifa wa Nahor.”