Far 24:20-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sai nan da nan ta bulbule tulunta a cikin kwami, ta sāke sheƙawa a guje zuwa rijiyar, ta kuwa ɗebo wa raƙumansa duka.

21. Mutumin kuwa ya zura mata ido, shiru, yana so ya sani ko Allah ya arzuta tafiyarsa, ko kuwa babu?

22. Sa'ad da raƙuman suka gama sha, mutumin ya ɗauki zoben zinariya mai nauyin rabin shekel, ya sa mata a hanci. Ya kuma ɗauki mundaye biyu na shekel goma na zinariya ya sa a hannuwanta,

23. ya ce, “Ki faɗa mini ke 'yar gidan wace ce? Akwai masauki a gidan mahaifinki inda za mu sauka?”

24. Sai ta ce masa, “Ni 'yar Betuwel ce ɗan Milka wanda ta haifa wa Nahor.”

25. Ta ƙara da cewa, “Muna da isasshen baro da harawa duka, da kuma masauki.”

26. Mutumin ya yi ruku'u ya yi wa Ubangiji sujada,

27. ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa ga maigidana ba. Ubangiji ya bi da ni har zuwa gidan ɗan'uwan maigidana.”

28. Budurwar ta sheƙa a guje zuwa gida wurin mahaifiyarta ta faɗi waɗannan abubuwa.

29. Rifkatu kuwa tana da ɗan'uwa sunansa Laban. Sai Laban ya sheƙo zuwa wurin mutumin a bakin rijiya.

30. Sa'ad da ya ga zoben da mundaye da suke hannuwan 'yar'uwarsa, sa'ad da kuma ya ji maganar Rifkatu 'yar'uwarsa cewa, “Ga abin da mutumin ya faɗa mini,” sai ya je wurin. Ya kuwa same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar.

31. Ya ce masa, “Shigo, ya mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.”

Far 24