1. Yanzu Ibrahim ya tsufa, ya kuwa kwana biyu. Ubangiji kuma ya sa wa Ibrahim albarka a cikin abu duka.
2. Ibrahim ya ce wa baransa, daɗaɗɗen gidansa wanda yake hukunta dukan abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata,
3. ka rantse da Ubangiji na sama da duniya, cewa ba za ka auro wa ɗana mata daga 'yan matan Kan'aniyawa waɗanda nake zaune a tsakaninsu ba.
4. Amma za ka tafi ƙasata, daga cikin dangina ka auro wa ɗana Ishaku mata.”