1. Ubangiji ya yi wa Saratu alheri kamar yadda ya alkawarta.
2. Saratu kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Ibrahim ɗa cikin tsufansa a lokacin nan da Allah ya faɗa masa.
3. Sai Ibrahim ya raɗa wa ɗansa wanda Saratu ta haifa masa, suna, Ishaku.
4. Ibrahim ya yi wa Ishaku ɗansa kaciya yana da kwana takwas, kamar yadda Allah ya umarce shi.
5. Ibrahim kuwa yana da shekara ɗari sa'ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku.
6. Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, har dukan wanda ya ji zai yi dariya tare da ni.”
7. Ta kuma ce, “Dā wa zai iya ce wa Ibrahim Saratu za ta bai wa 'ya'ya mama? Duk da haka cikin tsufansa na haifa masa ɗa.”
8. Yaron ya yi girma, aka yaye shi, Ibrahim kuwa ya yi babban biki a ranar da aka yaye Ishaku.