4. “Wannan shi ne alkawarin da zan yi maka, za ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa.
5. Ba za a ƙara kiran sunanka Abram ba, amma sunanka zai zama Ibrahim, gama na sa ka, ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa.
6. Zan arzuta ka ainun, daga gare ka zan yi al'ummai, daga gare ka kuma sarakuna za su fito.
7. “Zan kafa alkawarina da kai, da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu, madawwamin alkawari ke nan, in zama Allahnka da na zuriyarka a bayanka.