15. Allah ya ce wa Ibrahim, “Ga zancen matarka Saraya, ba za ka kira sunanta Saraya ba, amma Saratu ne sunanta.
16. Zan sa mata albarka, banda haka kuma zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za ta kuwa zama mahaifiyar al'ummai, sarakunan jama'a za su fito daga gare ta.”
17. Sai Ibrahim ya yi ruku'u, ya yi dariya a zuciyarsa, ya ce wa kansa, “Za a haifa wa mai shekara ɗari ɗa? Zai yiwu Saratu mai shekara tasa'in ta haifi ɗa?”
18. Sai Ibrahim ya ce wa Allah, “Da ma dai a bar Isma'ilu kawai ya rayu a gabanka.”
19. Allah ya ce, “A'a, matarka Saratu ita ce za ta haifa maka ɗa, za ka raɗa masa suna Ishaku. A gare shi zan tsai da alkawarina madawwami, da kuma ga zuriyarsa a bayansa.
20. Ga zancen Isma'ilu kuwa, na ji, ga shi, zan sa masa albarka in kuma riɓaɓɓanya shi ainun. Zai zama mahaifin 'ya'yan sarakuna goma sha biyu, zan maishe shi al'umma mai girma.
21. Amma ga Ishaku ne zan tsai da alkawarina, wato wanda Saratu za ta haifa maka a baɗi war haka.”
22. Sa'ad da Allah ya gama magana da Ibrahim, sai ya tafi ya bar Ibrahim.
23. Ibrahim kuwa ya ɗauki Isma'ilu ɗansa, da dukan bayi, haifaffun gidansa, da waɗanda aka sayo su da kuɗinsa, ya kuwa yi wa kowane namiji na jama'ar gidansa kaciyar loɓarsa a wannan rana bisa ga faɗar Allah.
24. Ibrahim na da shekara tasa'in da tara sa'ad da aka yi masa kaciyar loɓarsa.
25. Isma'ilu ɗansa yana ɗan shekara goma sha uku sa'ad da aka yi masa kaciya.
26. A wannan rana, Ibrahim da ɗansa Isma'ilu aka yi musu kaciya,
27. da mazajen gidansa duka, da waɗanda suke haifaffun gidan da waɗanda aka sayo da kuɗi daga baƙi, aka yi musu kaciya tare da shi.