Far 17:11-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Loɓarku za ku yanke, don alamar alkawari a tsakanina da ku.

12. Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan tsararrakinku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba.

13. Duka biyu, da wanda aka haifa daga gidanka, da wanda ka saya da kuɗi, za a yi musu kaciya. Da haka alkawarina zai kasance cikin jikinku, madawwamin alkawari ke nan.

14. Kowane ɗa namiji da bai yi kaciya ba, wato wanda bai yi kaciyar loɓarsa ba, za a fitar da shi daga jama'arsa, don ya ta da alkawarina.”

15. Allah ya ce wa Ibrahim, “Ga zancen matarka Saraya, ba za ka kira sunanta Saraya ba, amma Saratu ne sunanta.

Far 17