Far 17:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A lokacin da Abram yake da shekara tasa'in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili.

2. Zan yi maka alkawari, in ba ka zuriya mai yawa.”

3. Sai Abram ya yi ruku'u, Allah kuwa ya ce masa,

4. “Wannan shi ne alkawarin da zan yi maka, za ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa.

5. Ba za a ƙara kiran sunanka Abram ba, amma sunanka zai zama Ibrahim, gama na sa ka, ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa.

Far 17