Sai Saraya ta ce wa Abram, “To, ga shi, Ubangiji ya hana mini haihuwar 'ya'ya. Shiga wurin baranyata, mai yiwuwa ne in sami 'ya'ya daga gare ta.” Abram kuwa ya saurari murya matarsa Saraya.