Muna sanar da sarki, cewa mun tafi lardin Yahuza a wurin Haikalin Allah Mai Girma. Ana ginin Haikalin da manyan duwatsu, ana kuma sa katakai a bango. Aikin yana ci gaba sosai a hannunsu.