Ez 45:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Wannan zai zama yankin ƙasarsa a cikin Isra'ila. Sarakunana kuma ba za su ƙara zaluntar mutanena ba, amma za su ba mutanen Isra'ila ƙasar bisa ga kabilansu.”

9. “Ni Ubangiji Allah na ce ku sarakunan Isra'ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari'a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, ni Ubangiji Allah na faɗa.

10. “Sai ku kasance da ma'aunai na gaskiya, kamar su mudu da garwa.

11. “Kwanon awo na mudu da na garwa girmansu ɗaya ne. Garwa goma ganga guda ne. Ganga ita ce za ta zama fitaccen ma'auni.

12. “Shekel zai zama gera ashirin. Mainanku ɗaya zai zama shekel sittin.”

13. “Wannan ita ce bayarwar da za ku yi. Za ku ba da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta alkama, da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta sha'ir.

14. Za ku ba da ɗaya daga cikin goma ta garwa daga kowace ganga ta mai. Ganga tana cin garwa goma.

15. Za ku ba da tunkiya ɗaya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu, a cikin Isra'ila.“Waɗannan su ne hadayu na gari, da na ƙonawa, da na salama, domin a yi musu kafara, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16. “Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwar domin Sarkin Isra'ila.

Ez 45