3. A cikin yanki mai tsarki za ka auna tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], da faɗi kamu dubu goma [10,000], inda Wuri Mafi Tsarki zai kasance.
4. Wannan yanki shi ne zai zama wuri mai tsarki na ƙasar. Zai zama na firistoci waɗanda suke hidima a cikin Haikali, waɗanda suke kusatar Ubangiji don su yi masa hidima. Wurin zai zama wurin gina gidajensu da kuma wuri mai tsarki domin Haikalin.
5. Wani sashi kuma mai tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], da faɗi kamu dubu goma [10,000], zai zama na Lawiyawa masu hidima cikin Haikalin, zai zama wurin da za su mallaka, su zauna a ciki.