Ez 45:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Sa'ad da kuka rarraba ƙasar gādo, sai ku keɓe wa Ubangiji wani wuri domin ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗinsa kuwa kamu dubu goma [10,000]. Dukan yankin zai zama wuri mai tsarki.

2. Daga cikin wannan, murabba'i mai tsawo kamu ɗari biyar, da faɗi ɗari biyar, zai zama wuri mai tsarki, fili kuma mai kamu hamsin zai kewaye wurin nan mai tsarki.

3. A cikin yanki mai tsarki za ka auna tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], da faɗi kamu dubu goma [10,000], inda Wuri Mafi Tsarki zai kasance.

4. Wannan yanki shi ne zai zama wuri mai tsarki na ƙasar. Zai zama na firistoci waɗanda suke hidima a cikin Haikali, waɗanda suke kusatar Ubangiji don su yi masa hidima. Wurin zai zama wurin gina gidajensu da kuma wuri mai tsarki domin Haikalin.

5. Wani sashi kuma mai tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], da faɗi kamu dubu goma [10,000], zai zama na Lawiyawa masu hidima cikin Haikalin, zai zama wurin da za su mallaka, su zauna a ciki.

Ez 45