2. “Ɗan mutum, ka fuskanci Fir'auna Sarkin Masar, ka yi annabci gāba da shi da dukan Masar.
3. Ka yi magana, ka ce, Ubangiji Allah ya ce,‘Ga shi, ina gāba da kai, kai Fir'auna Sarkin Masar,Babban mugun dabba wanda yake kwance a tsakiyar koguna,Wanda yake cewa, Kogin Nilu naka ne, kai ka yi shi.
4. Zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka,In kuma sa kifayen kogunanka su manne a ƙamborinka,Zan jawo ka daga cikin tsakiyar kogunanka,Da dukan kifayen kogunanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,
5. Zan yashe ka, kai da dukan kifayen kogunanka cikin jeji.Za ka fāɗi a fili, ba kuwa wanda zai ɗauke ka, ya binne ka.Zan sa ka zama abincin namomin jeji da tsuntsayen sararin sama.
6. A sa'an nan mazaunan Masar za su sani ni ne Ubangiji,Domin sun zama wa mutanenIsra'ila kamar sandan iwa.