Ez 27:28-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Saboda kukan masu ja miki gora, ƙasa ta girgiza.

29. “ ‘Daga cikin jiragen ruwansu dukan waɗanda suke riƙe da matuƙi za su zo.Matuƙan jiragen ruwa da masu jagora za su tsaya a gaɓar teku.

30. Za su yi kuka mai zafi dominki.Za su yi hurwa, su yi birgima cikin toka.

31. Za su aske kansu saboda ke, su sa tufafin makoki.Za su yi kuka mai zafi dominki.

32. A cikin makokinsu dominki, suna kuka, suna cewa,Wa yake kama da Taya,Ita wadda take shiru a tsakiyar teku?

33. Sa'ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi,Kin wadatar da al'ummai,Kin arzuta sarakunan duniya da yawan dukiyarki da hajarki.

Ez 27