13. “‘Ga shi, na tafa hannuna saboda ƙazamar riba da ka ci, da jinin da ka zubar.
14. Zuciyarka za ta iya ɗaurewa, hannuwanka kuma za su ƙarfafa a ranar da zan gamu da kai? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.
15. Zan watsar da kai cikin al'ummai, in warwatsa ka cikin ƙasashe, zan kawo ƙarshen mugayen ayyukanka.
16. Za a ƙasƙantar da kai a gaban sauran al'umma, sa'an nan za ka sani ni ne Ubangiji.”’
17. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
18. “Ɗan mutum, mutanen Isra'ila sun zama kamar ƙwan maƙera a gare ni. Dukansu sun zama kamar tagulla, da kuza, da baƙin ƙarfe, da darma, a tanderu, sun zama ƙwan maƙera na azurfa.
19. Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce da yake dukanku kun zama ƙwan maƙera zan tattara dukanku a Urushalima.
20. Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da darma, da kuza a cikin tanderu, su hura wuta a kansu, don su narkar da su, haka zan tattara ku da zafin fushina in narkar da ku.
21. Zan tattaro ku, in hura muku wutar hasalata, za ku narke a cikinta.
22. Kamar yadda azurfa takan narke a cikin tanderu, haka kuma za ku narke, za ku sani ni, Ubangiji ne, na zubo muku da zafin fushina.”