1. “Sai ka yi makoki domin hakiman Isra'ila,
2. Ka ce, ‘Mahaifiyarka zakanya ce a cikin zakoki,Ta yi zamanta tare da 'yan zakoki,Ta yi renon kwiyakwiyanta.
3. Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta,Ya zama sagari,Sai ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.
4. Da al'ummai suka ji labarinsa,Sai suka kama shi cikin wushefensu,Suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa Masar.
5. Sa'ad da ta ga wanda ta sa zuciya a kansa ya tafi,Sai ta ɗauki ɗaya kuma daga cikin kwiyakwiyanta,Ta goye shi ya zama sagari.
6. Sai ya yi ta kai da kawowa a cikin zakoki,Ya zama sagari,Ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.
7. Ya lalatar da kagaransu,Ya mai da biranensu kufai,Ƙasar da waɗanda suke cikinta suka tsorata da jin rurinsa.
8. Sai al'ummai suka kafa masa tarko a kowane waje,Sun kafa masa tarko,Suka kama shi cikin wushefensu.