Ez 18:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Me kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra'ila cewa,‘Ubanni sun ci 'ya'yan inabi masu tsami,Hakoran 'ya'ya kuwa sun mutu’?

3. “Ni Ubangiji Allah na ce, hakika, ba za a ƙara faɗar wannan karin magana a Isra'ila ba.

Ez 18