1. A kan rana ta goma sha uku ga watan sha biyu, wato watan Adar, a ranar da za a aikata maganar sarki da dokarsa, wato a ranar da maƙiyan Yahudawa za su fāɗa musu, sai ranar ta zama ranar da Yahudawa ne za su tasar wa maƙiyansu.
2. Sai Yahudawa suka taru a biranensu a dukan lardunan sarki Ahasurus, don su tasar wa waɗanda suke so su yi musu ɓarna. Ba wanda ya tasar musu gama tsoronsu ya kama mutane.