Esta 8:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sa'an nan kuma Esta ta faɗi a wajen ƙafafun sarki, ta roƙe shi da hawaye ya kawar da mugun shirin da Haman Ba'agage ya shirya wa Yahudawa.

4. Sai sarki ya miƙo wa Esta sandan sarauta na zinariya.

5. Esta kuwa ta miƙe tsaye a gaban sarki, ta ce, “Idan sarki ya yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, idan ya yi wa sarki kyau, idan kuma sarki yana jin daɗina, bari a yi rubutu a soke wasiƙun da Haman Ba'agage ɗan Hammedata ya rubuta don a hallaka Yahudawan da suke cikin dukan lardunan sarki.

6. Gama ƙaƙa zan iya daurewa da ganin masifa da hallaka na mutanena da dangina?”

7. Sai sarki Ahasurus ya ce wa sarauniya da Mordekai, Bayahude, “Ga shi, na riga na ba Esta gidan Haman, an kuma riga an rataye shi a bisa gungume domin ya so ya taɓa Yahudawa.

8. Sai ku rubuta doka yadda kuke so da sunan sarki zuwa ga Yahudawa. Ku hatimce ta da hatimin zoben sarki, gama dokar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce ta da hatimin zoben sarki, ba za a iya a soke ta ba.”

Esta 8