3. Sai sarki ya ce, “To, wace irin daraja ko girma aka ba Mordekai saboda wannan?”Barorin sarki waɗanda suke yi masa hidima suka ce, “Ba a yi masa kome ba.”
4. Sarki kuwa ya ce, “Wane ne yake a shirayi?”Daidai lokacin ne kuwa Haman ya shigo shirayi na fari na fādar sarki, don ya yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a gungumen itace da ya shirya.
5. Barorin sarki suka ce, “Ai, Haman ne yake tsaye a shirayi.”Sai sarki ya ce ya shigo.
6. Da shigowar Haman, sai sarki ya ce masa, “Me za a yi wa mutumin da sarki yake so ya ɗaukaka?”Haman ya yi tunani ya ce a ransa, “Wane ne sarki yake so ya ɗaukaka, in banda ni?”