Dan 5:22-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. “Kai kuma Belshazzar, da kake ɗansa, ka san wannan duka, amma ba ka ƙasƙantar da kanka ba.

23. Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.

24. “Domin haka Allah ya aiko da wannan hannu da ya yi rubutun nan.

25. Wannan shi ne rubutun da aka yi, MENE, MENE, TEKEL, da UPHARSIN.

26. Ma'anar wannan ita ce, MENE, wato Allah ya sa kwanakin mulkinka su ƙare, sun kuwa ƙare.

27. Ma'anar TEKEL ita ce an auna ka a ma'auni, aka tarar ka kāsa.

28. Ma'anar PERES ita ce an raba mulkinka, an ba mutanen Mediya da na Farisa.”

29. Sai Belshazzar ya ba da umarni, aka sa wa Daniyel rigar shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku cikin masu mulkin ƙasar.

30. A wannan dare kuwa aka kashe Belshazzar Sarkin Kaldiyawa.

31. Dariyus kuwa Bamediye ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.

Dan 5