31. Sojojinsa za su ɓata tsattsarkan wuri da kagararsa. Za su kuma hana yin hadayu na yau da kullum, su kafa abin banƙyama da suke lalatarwa.
32. Waɗanda suka ta da alkawarin kuma, sarki zai ƙara dulmuyar da su ta wurin daɗin bakinsa. Amma waɗanda suka san Allahnsu za su tsaya da ƙarfi su yi wani abu.
33. Waɗansu daga cikin mutane waɗanda suke da hikima, za su wayar da kan mutane da yawa. Amma duk da haka za a kashe su da takobi, waɗansu da wuta, a washe waɗansu a kai su bauta.
34. Sa'ad da suka fāɗi ba za su sami wani taimakon kirki ba, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci.
35. Waɗanda suke da hikima, za a kāshe su, don a tsabtace su, a tsarkake su, su yi tsab tsab, har matuƙar da aka ƙayyade ta yi.
36. “Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.
37. Ba zai kula da gumakan kakanninsa ba, ko begen da mata suke yi. Ba kuwa zai kula da kowane irin gunki ba, domin zai aza kansa ya fi su duka.
38. A maimakon haka zai girmama gunkin kagarai, gunkin da kakanninsa ba su ko sani ba, shi ne zai miƙa masa zinariya, da azurfa, da duwatsu masu daraja, da abubuwa masu tamani.
39. Zai tasar wa kagara mafi ƙarfi da taimakon baƙon gunki. Waɗanda suka yarda da shi, zai ba su girma, ya kuma shugabantar da su a kan mutane da yawa, zai raba musu ƙasa ta zama ladansu.
40. “A lokaci na ƙarshe sarkin kudu zai tasar masa, sarkin arewa kuwa zai tunzura, ya tasar masa da karusai da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, ya ci su da yaƙi, ya wuce.
41. Zai shiga kyakkyawar ƙasa ya kashe dubban mutane. Amma ƙasar Edom, da ta Mowab, da yawancin ƙasar Ammonawa za su kuɓuta daga hannunsa.
42. Zai kai wa waɗansu ƙasashe yaƙi, ƙasar Masar kuwa ba za ta kuɓuta ba.
43. Zai mallaki dukiyoyi na zinariya, da na azurfa, da dukan abubuwa masu tamani na Masar. Zai kuma ci Libiyawa da Habasha da yaƙi.
44. Labarin da zai zo masa daga gabas da arewa zai firgita shi, shi kuwa zai ci gaba da yin yaƙi da zafi, ya karkashe mutane da yawa, ya shafe su.
45. Zai kafa manyan alfarwai na sarauta a tsakanin teku da tsattsarkan dutse. Amma zai mutu ba kuwa wanda zai taimake shi.”