Dan 11:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta fari ta sarautar Dariyus Bamediye, na tashi na tabbatar da shi, na kuma ƙarfafa shi.”

2. “Yanzu zan faɗa maka gaskiya. Za a ƙara samun sarakuna uku a Farisa, amma na huɗun zai fi dukansu dukiya. Sa'ad da ya ƙasaita saboda dukiyarsa, zai kuta dukan daularsa ta yi gaba da mulkin Hellas.

3. “Sa'an nan wani sarki babba zai taso wanda zai yi mulki da babban iko yadda ya ga dama.

Dan 11