14. Amma kai kana firgita ni da mafarkai,Kana aiko mini da wahayi da ganegane,
15. Har nakan fi so a rataye ni,Gara in mutu da in rayu a wannan hali.
16. Na fid da zuciya. Na gaji da rayuwa.Ku rabu da ni. Rayuwa ba ta da wata ma'ana.
17. “Ya Ubangiji, me ya sa mutum yake da daraja haka a gare ka?Me ya sa kake lura da abin da yake yi?
18. Kakan dube shi kowace safiya.Kana jarraba shi a kowane daƙiƙa.
19. Ba za ka ko ɗan kawar da kai ba,Don in samu in haɗiye yau?