Ayu 7:10-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ba kuwa zai ƙara komowa ba,Mutanen da suka san shi, duka za su manta da shi.

11. A'a, ko kaɗan ba zan yi shiru ba!Haushi nake ji, zuciyata ta ɓaci,Dole ne in yi magana.

12. “Ya Ubangiji, don me ka sa ni a waƙafi?Kana tsammani ni dodon ruwa ne?

13. Na kwanta ina ƙoƙari in huta,Ina neman taimako don azabar da nake sha.

14. Amma kai kana firgita ni da mafarkai,Kana aiko mini da wahayi da ganegane,

15. Har nakan fi so a rataye ni,Gara in mutu da in rayu a wannan hali.

16. Na fid da zuciya. Na gaji da rayuwa.Ku rabu da ni. Rayuwa ba ta da wata ma'ana.

Ayu 7