7. Ba na jin marmarin cin abinci irin haka,Kowane irin abu da na ci yakan sa mini cuta.
8. “Me ya sa Allah ya ƙi ba ni abin da nake roƙo?Me ya sa ya ƙi yin abin da nake so?
9. Da ma ya ci gaba kawai ya kashe ni,Ko ya sake ikonsa ya datse ni!
10. Da na san zai yi haka, da sai in yi tsalle don murna,Da ba zan kula da tsananin azabar da nake ciki ba.Ban taɓa yin gāba da umarnan Allah ba.